Kar ka damu da waɗanda suke fatan ganin gazawarka. Ka mayar da hankali kan ci gaba da neman nasararka, kuma idan ka samu nasara, ka yi amfani da damar da Allah ya ba ka don taimakawa mutane. Ka sani cewa A rayuwa, masu fatan ganin gazawarka ba su da muhimmanci idan ka mai da hankali kan manufarka da alkhairi.
Annabi صلى الله عليه وسلم yace; "Tabbas, mafi kusanci da Allah Subhanahu-Wa-Ta'ala shine wanda yafi sauran mutane wajen yada Sallama". Allah yasa mu kasance daga cikinsu. Ameen!
Ranar farko a gidan Aljanna, haƙiƙa za a ga ababan mamaki. Gidaje na alfarma. Ƙoramai na gudana. Ga Ƴaƴan itatuwa ko'ina. Ga Gadaje na Zinare. Lokaci ne da zaka haɗu da waɗanda kake ƘAUNA amma sun daɗe da mutuwa. Lokaci ne da IYAYE zasu sake haɗuwa da Ƴaƴansu kuma Lokaci ne da zaka ga Kakanni sun dawo yara wato cikin ƙuriciyarsu. Lokaci ne da za ka ga Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama kuma kaga Sahabbansa da duk Annabawa da Shahidai..! Lokaci ne da zaka ga Mala'iku da ƙwayar Idonka. Lokacin d zaka ga Ubangiji Ido da Ido kamar yadda kake ganin wata ɗan daren 14. Ya ya zaka ji a ranka idan ka ganka a gidan Aljanna bayan k gama shan wahalar Duniya. Bayan k gama tsallake jarrabawar Ƙabari da wahalarsa. An gama yi maka HISABI ka tsallake SIRAƊI....! Ya zaka ji bayan kana kallo ana jefa wasu a cikin JAHANNAMA amma kai ka kubuta..! Ƙunci, Damuwa, Hassada, Baƙin ciki duk sun ƙare. Ya zaka ji a ranka lokacin da mai kira ya yi kira y ce "Ya ku Ƴan Aljanna, zaku dawwama ...
Masha Allah
ReplyDeleteMasha Allah
Delete