Posts

Showing posts from August, 2024

HADAFIN RAYUWA

 Kar ka damu da waɗanda suke fatan ganin gazawarka.  Ka mayar da hankali kan ci gaba da neman nasararka, kuma idan ka samu nasara, ka yi amfani da damar da Allah ya ba ka don taimakawa mutane. Ka sani cewa A rayuwa, masu fatan ganin gazawarka ba su da muhimmanci idan ka mai da hankali kan manufarka da alkhairi.

RANAR FARKO A GIDAN ALJANNA

 Ranar farko a gidan Aljanna, haƙiƙa za a ga ababan mamaki. Gidaje na alfarma. Ƙoramai na gudana.  Ga Ƴaƴan itatuwa ko'ina. Ga Gadaje na Zinare. Lokaci ne da zaka haɗu da waɗanda kake ƘAUNA amma sun daɗe da mutuwa.  Lokaci ne da IYAYE zasu sake haɗuwa da Ƴaƴansu kuma Lokaci ne da zaka ga Kakanni sun dawo yara wato cikin ƙuriciyarsu. Lokaci ne da za ka ga Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama kuma kaga Sahabbansa da duk Annabawa da Shahidai..! Lokaci ne da zaka ga Mala'iku da ƙwayar Idonka. Lokacin d zaka ga Ubangiji Ido da Ido kamar yadda kake ganin wata ɗan daren 14. Ya ya zaka ji a ranka idan ka ganka a gidan Aljanna bayan k gama shan wahalar Duniya. Bayan k gama tsallake jarrabawar Ƙabari da wahalarsa. An gama yi maka HISABI ka tsallake SIRAƊI....! Ya zaka ji bayan kana kallo ana jefa wasu a cikin JAHANNAMA amma kai ka kubuta..! Ƙunci, Damuwa, Hassada, Baƙin ciki  duk sun ƙare. Ya zaka ji a ranka lokacin da mai kira ya yi kira y ce "Ya ku Ƴan Aljanna, zaku dawwama ...

HADITH

 Annabi  صلى الله عليه وسلم yace; "Tabbas, mafi kusanci da Allah Subhanahu-Wa-Ta'ala shine wanda yafi sauran mutane wajen yada Sallama".   Allah yasa mu kasance daga cikinsu.  Ameen!

ILIMI CIKIN RAYUWA

Image
 Rayuwar da kake Korafi Akai, Ita ce rayuwar da wani ke Nema. Ka zamo Mai Godiya ga Allah. #lifestyle#struggle#LeadershipDevelopment

SAKON GODIYA

Image
  Ina Mika Sakon Godiya ga Dukkan Al'umar kasa ta Najeriya da Kuma Musulman Duniya Wajen bani Hadin Kai da nuna goyon baya Domin tabbatar da wannan kafa tawa. Nagode sosaii, Allah ya saka muku da Alkhairi💯 Sulaiman A Wangarawa.

ALHAMDULILLAH

 Alhamdulillah Dukkan Godiya ta Tabbata ga Ubangiji Madaukacin Sarki, Tsira da Aminci Su Tabbata ga Fiyayyen Halittah Annabi Muhammad (S.A.W?.