Ranar farko a gidan Aljanna, haƙiƙa za a ga ababan mamaki. Gidaje na alfarma. Ƙoramai na gudana. Ga Ƴaƴan itatuwa ko'ina. Ga Gadaje na Zinare. Lokaci ne da zaka haɗu da waɗanda kake ƘAUNA amma sun daɗe da mutuwa. Lokaci ne da IYAYE zasu sake haɗuwa da Ƴaƴansu kuma Lokaci ne da zaka ga Kakanni sun dawo yara wato cikin ƙuriciyarsu. Lokaci ne da za ka ga Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama kuma kaga Sahabbansa da duk Annabawa da Shahidai..! Lokaci ne da zaka ga Mala'iku da ƙwayar Idonka. Lokacin d zaka ga Ubangiji Ido da Ido kamar yadda kake ganin wata ɗan daren 14. Ya ya zaka ji a ranka idan ka ganka a gidan Aljanna bayan k gama shan wahalar Duniya. Bayan k gama tsallake jarrabawar Ƙabari da wahalarsa. An gama yi maka HISABI ka tsallake SIRAƊI....! Ya zaka ji bayan kana kallo ana jefa wasu a cikin JAHANNAMA amma kai ka kubuta..! Ƙunci, Damuwa, Hassada, Baƙin ciki duk sun ƙare. Ya zaka ji a ranka lokacin da mai kira ya yi kira y ce "Ya ku Ƴan Aljanna, zaku dawwama ...